Allura Ta Tono Garma Bayan An Gurfanar Da Matashin Da Ake Zargi Da Fisgo Hoton Alkalin Alkalai A Kotu.

Spread the love

Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Kasuwa Kano, karkashin jagorancin mai shari’a, Abdu Abdullahi Waiya, ta dage shari’ar matashin nan mai suna Ado Shehu ( Usman), bisa zargin sa da yunkurin kashe kansa da kuma fisgo hoton alkalin alkalai na jahar.

A ranar Larabar da ta gabata 18 ga watan Satumba 2024, wanda ake zargin ya shiga kotun shari’ar addinin musulinci ta CT Number 1, inda ya fisgo hoton Grand Khadin, a saman wajen zaman alkali sannan ya buga shi da kasa, da kuma yunkurin kashe kansa wai saboda kwanaki uku kenan bai ci abinci ba, inda jami’an yan sanda suka tafi da shi don fadada bincike akansa.

A zaman kotun na ranar Alhamis bayan an gurfanar da shi, kotun ta bayar da umarnin a mayar da wanda ake zargin, wajen jami’an yan sanda don ci ga bada da bincikarsa, sakamakon korafe-korafe da aka shigar akansa.

Kakakin manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya shaida wa Idongari.ng, cewa kafin matashin ya je kotun CT number 1, ya fara zuwa wata babbar kotun shari’ar addinin musulinci, inda ya yi wa alkalin karyar cewa zai kashe kansa domin rayuwa ta yi masa tsanani, amma aka yi masa nasiha tare da taimaka masa da kudade ciki harda wadanda Lauyoyi suka tallafa masa.

Haka zalika ana zargin abaya ya shiga kasuwar Kwari Kano, inda ya bayyana wa yan kasuwar cewar shi kirista ne amma ya musulinta, har suka tallafa masa da makudan kudade.

To sai dai Muzammil fagge, ya kara da cewa shi kansa ya gane wanda ake zargin domin abaya ya taba zuwa wani gidan Radio, da suke gabatar da shiri har ya yi korafi kuma aka tallafa masa, har aka yi masa aure amma ya kwashe kayan dakin matarsa ya siyar sannan ya gudu ya barta.

‘’ Mu tausaya masa al’umma sun tausaya masa domin an tallafa masa ta ko’ina ‘’.

Shima matashin da ake zargi, Shehu Ado wato Usman , ya tabbatar da cewar ya aikata laifin kuma yanzu abun yana damunsa a koda yaushe.

Fagge, ya shawarci al’umma da su dinga bincike kafin su taimaka wa, mutum don kaucewa yaudara da cuta, inda ya ce wannan matashin ya mayar da abun tamkar sana’a kuma ba za su yadda da irin wannan lamari ba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *