Al’umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP

Spread the love

Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo.

Wani mazaunin garin da ya gudu daga al’ummarsa zuwa Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.

A yayin da ya ke bayar da labarin yadda lamarin yake, mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su.

A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno.

Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefen tafkin Chadi wadda ta shahara wajen kamun kifi da noma, kuma akwai dakarun sojojin Najeriya da na ruwa.

Duk da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, mayaƙan Boko Haram/ISWAP na ci gaba da kai hare-hare a cikin al’ummomin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *