Al’umma Su Ci Gaba Da Aikata Aiyukan Alkairi: Dagacin Yankusa.

Spread the love

An Shawarci Al’ummar musulmi da su ci gaba da aikata ayyukan Alkhairi, domin samun sakamakon me kyau a Duniya da Lahira.

Dagacin garin Yankusa dake yankin karamar hukumar Kumbotso Alhaji Bala Isa Yankusa ne,  ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilin jaridar idongari.ng, inda ya yi kira da al’ummar musulmi da su ci gaba da taimakawa marayu da marasa karfi da sana’oin dogaro dakai.

Dagacin garin Yankusa ya ƙara da cewa, yin ayyuka mai kyau yana da matuƙar amfani, domin za’a yi wa kowanne rai hisabi game da ayyukan da yayi a ranar Lahira.

Alhaji Bala Isa Yankusa ya shawarci Matasa da su nemi ilimin Al-qur’ani da na boko, domin samun nasara a rayuwar su a kowanne mataki.

Ya ce  watan ramadan wata makaranta ce ta musamman, inda ya yi kira ga Musulmi da su ci-gaba da aikata ayyukan alkhairi koda bayan wuce war Watan.

Ya kuma sanar da cewa za’a sallah idi a masallacin idi na garin Yankusa da misalin karfe 8:30 inda yayi kira da al’ummar musulmi su fito cikin nutsuwa tare da koyi da sunnar annabi ( SAW) ya yi zuwa masallacin idi

A ƙarshe ya yi kira ga jama’a da su ci-gaba da bada goyon bayan su, ga shirye-shiryen gwamnantin domin samun ayyukan ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *