Al’umma Sun Gabatar Da Saukar Alkur’ani Mai Girma Da Addu’o’i Ga Tsohon Shugaban DSS Yusuf Bichi.

Spread the love

Al’ummar karamar hukumar Bichi sun gudanar da saukar al’qur’ani mai girma tare da yin addu’o’i na musamman domin yin godiya ga Allah (S W T) bisa yadda ya nufi tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS Malam Yusuf Magaji Bichi ya kammala aiki lafiya.

Rahotanni na cewa Limamai, Alarammomi da al’ummar garin Bichi ne suka taru a Babban Masallacin Juma’a dake Bichi domin gudanar Saukar karatun Alqur’ani .ai girma tare da addu’o’i na musamman .

A yayin taron addu’ar Wanda Limamai da Alarammomin sun roki Allah SWA ya kara baiwa Malam Yusuf Magaji wata dama sama da ta baya da kuma ya kammala aikin lafiya.

Haka kuma an gabatar da addu’ar ga Mai dakisa Hajiya Aisha Uwar Marayu bisa yadda take taimako marasa gata tare da addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya da dorewar tatttalin arziki ga karamar Hukumar Bichi, jihar Kano dama Kasa baki daya.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Taro ya Sami halatar Jama’a da dama cikin harda Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarrayya dake garin Dutsi-ma a Jahar Katsina Ferfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar litinin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke Malam Yusuf Magaji Bichi daga mukamin Babban Darakta na DSS bayan shafe sama da shekaru 5 yana jagorantar hukumar.

Shugaban Kasar ya godewa Bichi bisa namijin kokarin da yayi wajen inganta aiyukan hukumar da Kuma samar da walwala ga ma’aikatan hukumar.

Al’ummar jihar kano dai sun jima suna yabawa Yusuf Magaji Bichi bisa yadda ya dauki matasa maza da Mata aikin DSS a jihar, Wanda ake ganin ba a taba samun wani Dan kano da ya samar da aikin yi ga matasa masu tarin yawa a jihar ba.

KADAURA24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *