Al’umma Sun Yi Murna Da Simamen Da Hukumar Hisbah Ta Kai Wani Gida A Unguwar Gaida Kano.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta yi nasarar kama wa su matasa su 6, a unguwar Gaida dake karamar hukumar Kumbotso, bisa zarginsu harkar Daudu da kuma neman maza.

Idonagri.ng, ta ruwaito cewa, kamen ya biyo bayan koken da al’ummar yankin suka yi ga hukumar Hisbar, akan wani gida da suke zargin ana aikata badala a cikinsa tsawon lokaci.

Hukumar Hisbar ta kai sumamen ne cikin dare, inda ta kamo matasa su 6 , wadanda dukkansu maza ne, kuma ana zarginsu da aikata badala.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da aikata amma sun nemi afuwar hukumar da kuma al’ummar yankin da cewa ba za su sake aikata wa ba.

A zantawarsu da Idongari.ng, sun tabbatar da cewa ana biyan kudi ne, daga naira 5000 har zuwa 50.000.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubukar , ya bayyana cewa da zarar sun kammala gudanar da bincike za su dauki matakin da ya dace akan matasan.

Saurari wannan muryar ..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *