Al’ummar Ogurute Oombe sun miƙa sabon asibiti ga gumaka don samun kariya a Enugu

Spread the love

Al’ummar garin Ogurute Oombe da ke jihar Enugu sun mika sabon asibitin da suka gina ga gumakansu domin samun kariya.

Wannan shawarar dai ta zo ne biyo bayan yawaitar satar kayan aikin asibitin a lokacin da ake gina shi.

A wani faifan bidiyo da BBC Igbo ta samu, wakilin al’ummar Ogurute Oombe ya bayyana takaicin mutanen kauyen tare da bayyana irin asarar da aka yi.

Kayayyakin da aka sace sun hada da motar daukar marasa lafiya da na’urar talabijin da injin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da sauran muhimman kayayyakin aiki da na’urorin da suka dace don gudanar da ayyukan asibitin.

“Mutanen da suke nan a yau ‘yan asalin garin Ogurute Oombe ne, kuma wannan shi ne babban asibitin Ogurute Oombe da gwamnati ta gina mana,” in ji kakakin.

“Gwamnati ta kawo mana kayayyakin da za mu yi amfani da su wajen kula da marasa lafiya, sun kawo injinan wutar lantarki mai amfani da hasken rana da motar daukar marasa lafiya da na’urar talabijin, da sauran abubuwa masu kyau da za ku iya tunani a kai.”

Ya ci gaba da cewa, “Amma yanzu babu wanda ya ga waɗannan kayayyakin aikin cikin kankanin lokaci bayan an kawo su, ba mu ji dadin hakan ba.”

Satar da aka yi ba wai kawai ta hana asibitin samun kayan aiki masu mahimmanci ba, har ma da kashe wa al’ummar fatar da suka sa rai da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

Dangane da irin wadannan sace-sacen da ake ta yi ne mutanen ƙauyen suka yanke shawarar neman kariya daga gumakansu da suke bautawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *