Alƙaliyar da ɗan sanda ya harba a kotun Kenyan ta mutu

Spread the love

Alƙalin Alƙalan Kenya ya ce alƙaliyar da ɗan sanda ya harba a lokacin da take tsaka da jagorantar shari’a a mutu a asibiti.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Justice Martha K Koome ya ce alƙaliyar kotun Makadara, Mai shiari’a Monica Kivuti ta “rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu”.

A ranar Alhamis ne wani babban jami’in ɗan sanda ya harbi Ms Kivuti a tsakiyar kotun, lokacin da ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da belin matarsa.

Bayan buɗe wa alƙaliyar wuta ne, ‘yan sandan ta ke ganin kotun suka mayar wa jami’in ɗan sandan mai suna Samson Kipchirchir Kipruto martani, inda suka kashe shi bayan harbin da suka yi masa.

Musayar wutar da ‘yan sandan suka yi da shi ta sa uku daga ciki sun samu raunuka, inda suka karɓar magani a asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *