Ambaliya: Kafafen Yada Labarai Suna Da Rawar Taka Wa Don Sake Gina Maiduguri, Sani Zorro.

Spread the love

Tsohon shugaban kungiyar yan jaridun Nigeria, Hon.Sani Zoro, ya yi kira ga kafafen yada labarai da su jagoranci yunkurin sake gina birnin Maiduguri dake jahar Borno, wanda ambaliyar ruwa ta mamaye birnin.

Zoro ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake  tattauna wa da manemalabarai  a birnin Kano.

Ya ce hakan yana da mutukar muhimmanci idan aka yi la’akari da rawar da kafafen yada labarai ke da shi, wajen samar da tallafi daga kungiyoyi, kamfanoni da kuma ma su hannu da shuni a lokutan daban-daban.

Sani Zoro , tsohon shugaban kwamitin majalissar wakilai ne, kan yan gudun hijira , bakin haure ya bayyana ambaliyar a matsayin abin takaici, bayan ballewar Dam din Alau, da ya shfi sama da mutane 239,000.

Ya kuma bayyana bala’in a matsayin mafi muni a cikin sama da shekaru 30, inda ya ce lamarin ya tayar da hankulan mazauna Maiduguri, tare da lalata kashi 40 cikin 100 na amfanin Gona da hakan ya kara ta’azzara matsalar karancin abinci da tsadar sa.

Ya kara jaddada bukatar kafafen yada labarai su ci gaba da bayyana halin da wadanda lamarin ya shafa don saukaka mu su da kuma gyara mu su gidajensu.

Tsohon dan majalissar ya bukaci ma su ruwa da tsaki da su hada kai wajen bayar da tallafin da ya dace, don rage mu su radadi, kuma a gaggauta samar mu su da matsuguni, abinci magunguna da kayayyakin ilimi .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *