Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 31 tare da rusa gida 5,000 a jihar Kano

Spread the love

Aƙalla mutum 31 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auka wa ƙananan hukumomin jihar Kano 21, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.

Babban sakatare na hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa reshen Kano, Isyaku Kubarachi, ya ce ambaliyar ta kuma rusa gidaje 5,280 a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

 

“Mutum 31,818 lamarin ya shafa da kuma rusa gidaje 5,280,” in ji shi. “Bala’in ya kuma lalata gonaki 2,518 da suka kai faɗin hekta 976.”

Ya ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya jawo ambaliyar, kuma akasarin gidajen da lamarin ya shafa na ƙasa ne.

One thought on “Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 31 tare da rusa gida 5,000 a jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *