Hukumar kula da jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Somaliya ya kai 110.
Hukumar ta ƙara da cewa sama da mutane miliyan ɗaya ne suka rasa matsugunansu sannan kuma mutane miliyan 2.4 ne suka sami ɓarna a yankuna 36.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin cewa akwai yiwuwar kamuwa da cututtuka da dama sakamakon rahotannin ɓarkewar cutar kwalara a jihohin Hirshabeelle da Galmudug.
Hukumar ta ƙara da cewa kashi 30 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa ne kawai suka samu taimako, amma an tura aƙalla jiragen ruwa 37 domin kai kayayyaki ko kuma kwashe waɗanda ruwan ya rutsa da su.
A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, Somaliya da makwabciyarta Kenya da Habasha sun fuskanci ruwan sama mafi yawa cikin fiye da shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya haddasa asarar rayuka, da matsugunai da kuma barna.