Tsohon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shigar wata fadar sarki da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano.
Da asubahin yau ne dai tsohon sarkin ya koma birnin tun bayan sanar da matakin tuɓe shi da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi ranar Alhamis.
Tun a cikin daren ne dai sarki Muhammadu Sanusi ll ya koma babbar fadar sarkin da ke cikin birni, tare da rakiyar gwamnan da sauran muƙarraban gwamnati.
To sai dai bayan komawar Aminu Ado birnin, bayanai sun ce ya koma wata ƙaramar fadar sarki da ke unguwar Nassarawa.
Tuni dai gwamnan jihar ya bai wa kwamishinan ‘yan sanda na jihar umarnin kama Alhaji Aminu Ado, kan abin da ya kira ”yunƙurin tayar da tarzoma” a birnin.
- Mun dauki kaddara game da masarautar mu da aka rushe’
- Sojojin Najeriya sun kama ‘masu kai wa’ ƴan tawayen Kamaru man fetur