Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ta Amnesty International ta ce dole ne sukan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saki dukkanin waɗanda aka kama a kan zanga-zangar tsadar rayuwa.
Da yake martani kan batun komawa shari’ar masu zanga-zangar da aka yi a wata babbar kotun tarayya jiya a Abuja, darektan ƙungiyar a Najeriya Isa Sanusi, ya ce dole ne shugaban ƙasar ya saki dukkanin waɗanda aka kama a kan zanga-zangar kuma ba tare da wani sharaɗi ba.
Ya ce tsare mutanen tun watan Agusta saboda kawai sun yi amfani da dama da ‘yancinsu na zanga-zangar lumana tare da tuhumarsu da laifuka na ban mamaki da suka haɗa da cin amanar ƙasa da ta’addanci ya nuna yadda gwamnatin Najeriya ba ta mutunta ‘yancin ɗan’Adam.
- Gurfanar Da ƙananan Yara A Gaban Kotu Tsantsar Zalunci Ne — Atiku.
- Tsananin Yunwa Da Wuya Ta Sanya Yaran Da Ake Zargi Da Zanga-zangar Yunwa Sun Suma A Kotu.
Darektan ya ce masu zanga-zangar 114 da aka gurfanar a kotun ba su yi wani abu da ya saɓa doka ba, kuma ba su cancanci irin muzgunawar da aka yi musu ba tun daga lokacin da aka kama su
Ya ce daga cikin mutum 76 da aka fara gabatarwa a kotun a jiya, yawancinsu yara ne, kuma faɗuwar hudu daga cikinsu a kotu alama ce da ta nuna mummunan yanayin da lafiyarsu ke ciki.
Shugaban ƙungiyar ta Amnesty ya ce tsare yara a irin wannan yanayi na tashin hankali a kan ƙin amincewarsu tare da neman mulki na gari ya nuna kudurin gwamnati na murƙushe masu suka.