Ofishin jakadancin kasar Amurika ya horas da jami’an Yan Sandan jihar Kano, dabarun yadda za su gane kudade masu kyau da kuma na jabu, sakamakon yada ake samun wasu batagarin mutane suna buga jabun takaddun kudaden kasashen daban-daban don damfarar jama’a.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wannan horon ya biyo bayan Wani bincike da ake Yi kan wasu matasa Uku, da ake zargi da mallakar kudaden jabun kasashen ketare da suka haura naira biliyan 129.
An karshen shekarar da ta gaba ne aka kama wadanda mutanen a lokacin da suke kokarin chanza kudaden daga Dalar Amurika zuwa kudin Nigeria wato Naira.
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa, masu bayar da horon dun gana jami’an da suke gudanar da bincike a shelkwatar Rundunar dake unguwar Bompai Kano tare da ba su horo na musamman kan yadda za su gane duk Wani kudi Mai kyau da kuma mara kyau.
Sauran sassan da aka horas sun hada da sashin kula da safarar kudi ba bisa ka’ida ba da sashin yaki da Damfara ta yanar gizo da daidai sauransu.
Ofishin jakadancin kasar Amurika ya ba wa rundunar ƴan sandan Kano, kayan aiki Kyauta, wadanda za su Yi amfani da su wajen gano kudaden jabu cikin sauki.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya godewa ofishin jakadancin kasar Amurikan, bisa horon da suka ba wa jami’an Yan Sandan da kuma kayan aikin da suka ba su, don ci gaba da tsaftace harkokin kasuwanci a fadin jihar Baki daya.
A karshe rundunar ƴan sandan ta lashi takobin ci gaba da kakkabe aiyukan batagari tare da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyin su.