Amurka ta ƙaƙaba wa editocin gidan talabijin ɗin RT na Rasha takunkumai

Spread the love

Gwamnatin Amurka ta sanar da ƙaƙaba takunkumai kan wasu shugabannin kafar yada labaran kasar Rasha ta RT da wasu mutane da dama.

Amurkar ta zarge su da yunƙurin yin katsalandan a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamba.

Baitulmalin Amurka ta zargi wasu mutum 10 – ciki har da babbar editan RT Margarita Simonovna, da mataimakiyarta Elizaveta Yuryevna Brodskaia — da wasu kungiyoyi biyu da yunkurin shirya tafka maguɗi a zaɓen na watan Nuwamba mai zuwa.

Mataimakin babban mai shigar da ƙara na Amurka, Matthew Olsen, ya yi magana ne a wani taro na Kwamitin duba barazana ga zabe na Ma’aikatar Shari’a.

Ya ce: “Tuhume-tuhumen da aka yi yau sun zama abin tunatarwa cewa ma’aikatar shari’a ta ci gaba da yin tsayin daka wajen kare dimokuradiyyarmu daga katsalandan ɗin ƙasashen waje da kuma kare haƙƙin Amurkawa da ke cikin tsarin mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *