Amurka ta gayyaci ɓangarorin yaƙin Sudan zuwa sabuwar tattaunawa

Spread the love

Amurka ta gayyaci ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan don gudanar da wata tattaunawar tsagaita wuta, inda ta bayyana yawan mace-mace da wahalar da ake fuskanta a matsayin mummunan lamari.

Saudiyya ce za ta karɓi bakuncin bangare ɗaya na tattaunawar kuma za a sake yi a kasar Switzerland a wata mai zuwa.

Amurka na kira ga rundunar sojin Sudan da dakarun RSF da su fuskanci tattaunawar da kyakkawar niyya da nufin ceton rayuka, da dakatar da fadan da ake gwabzawa da samar da hanyar da za a bi wajen cimma yarjejeniya mai dorewa.

Wakilan Tarayyar Afirka da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya za su halarci tattaunawar a matsayin masu sa ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *