An ɗaure ɗan Najeriyan da ya damfari mutanen ƙasashe 13

Spread the love

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta samu wani mazambaci, Eze Harrison Arinze, da laifin damfarar mutum 34 a ƙasashe 13 kuɗin da ya kai $592,000.

Waɗanda ya damfara sun fito daga Burundi da Cameroon da Coasta Rica da Jamus da Ghana da Hungary da India da Rwanda da Singapore da Afirka ta Kudu da Uganda da Amurka da Zimbabwe.

Hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta’annati, EFCC ce ta gurfanar da Arinze gaban mai shari’a J.K Omotosho kan laifin da ya shafi yin sojan gona.

Arinze dai ya amsa laifinsa bayan da aka karanto masa uhumar da ake yi masa.

Lauyan mai gabatar da ƙara Christopher Mshelia ya nemi kotu ta yanke wa wanda ake tuhuma hukunci.

Mai shari’a Omotosho ya yanke wa Arinze hukuncin shekara uku a gidan yari da zaɓin biyan tara ta naira miliyan 3.

A baya-bayan nan, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce abin damuwa ne yadda kashi 70 cikin 100 na ɗaliban Najeriya ke aikata zamba ta intanet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *