An ƙara kashe ‘yansandan Najeriya shida a jihar Delta

Spread the love

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta tabbatar da kashe wasu jami’anta shida a jihar Delta.

A watan Janairu ne ‘yan bindiga suka sace wasu ‘yansanda uku da ke kan aiki, lokacin da aka kira su wani waje da ake hatsaniya a Ohoro cikin Ƙaramar Hukumar Ughelli ta arewa.

Jami’an uku na cikin tawagar ‘yansada shida da aka kai wajen duba ababan hawa a Ughelli kan titin Patani.

Makonni kaɗan aka sake kai wasu ‘yansandan domin ceto abokan aikinsu da aka sace.

Yayin wannan aiki ne aka yi wa ‘yansandan kofar rago aka kashe su a wajen dajin Ohoro da ke ƙaramar hukumar Ughelli.

Yan Bindiga Sun Saki Ɗaliban Kuriga

Yan Sandan Jahar Adamawa Sun Kama Matasa Uku Da Ake Zargi Da Aikata Fashin Wayoyin Al’umma

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, kakain ‘yansandan jihar Muyiwa Adejobi, ya ce an gano gawarwakin jami’an shida da aka kashe, ana kuma ci gaba da neman wasu jami’ai shida na daban.

“An gano gawar waɗannan jami’an ne lokacin da ake binciken haɗin gwiwa tsakanin ‘yansanda da sauran jami’an tsaro,” in ji Adejobi.

“Rundunarmu ta mayar da hankali wajen neman sauran jami’anmu shida, a gefe guda kuma mun tuntubi duka iyalansu kan wannan batu.

“Waɗanda suka mutu sun hada da Sifeto Abe Olubunmi da ya fara aiki 1 ga watan Agusta, 2003, Septo Friday Irorere 1 ga watan Janairun 2003, Sajan Kuden Elisha 17 ga watan oktoba 2011, Sajan Akpan Aniette shi ma 17 ga watan Oktoba 2011, Sajan Ayere Paul 17 ga Oktoba 2011, sai kuma Sajan Ejemito Friday wanda shi ma ya fara aiki 17 Oktoba 2011.

“Jami’an da ake ci gaba da nema kuma sun haɗa da Sefeto Onoja Daniel enlisted da Sefeto Onogho Felix da Sefeto Emmanuel Okoroafor enlisted da Sufeto Joel Hamidu.

“Akwai kuma Sajan Moses Eduvie da kuma Sajan Cyril Okorie,” in ji sanarwar

Ya ce za a yi bikin binne waɗannan jami’ai a Abuja ranar 5 ga watan Afrilu.

Ya zuwa yanzu an kama mutum biyar da ake zargi da hannu cikin kashe jami’an.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *