An ɗage sauraron ƙarar da Sarki Aminu Ado Bayero ya shigar

Spread the love

Babbar kotun tarayyar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, ya shigar da ƙara gabanta inda yake neman kotun ta hana kama shi, sannan kuma a mayar da shi gidan sarki na ƙofar kudu a matsayin sarkin Kano ta ɗage zamanta a yau Juma’a.

Kotun ta saurari ɓangarori biyu na shari’ar, inda masu ƙarar suka ƙara har da buƙatar take wa Sarki Aminu Ado haƙƙi da kuma neman kada wanda ya cuzguna masa.

Lauyan gwamatin jihar Kano, Mahmud Magaji ya yi suka kan wasu daga cikin buƙatun da masu ƙara suka nema, sannan ya nemi kotun ta yi watsi da su.

Alƙalin kotun Amobeda Simon ya ɗage zaman inda ya ce zai sanar da ranar da zai yanke hukunci a kan abubuwan da bangarorin biyu suka nema.

A ci gaba da wannan dambarwa ta masarautar ta Kano, ranar 11 ga watan nan na Yuni ne, ake sa ran babbar kotun jihar Kano za ta saurari ƙarar da sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya shigar inda yake neman jami’an tsaro da kada su kama shi ko aiwatar da duk wani nau’in cuzgunawa ko fitar da shi daga gidan sarki na Kofar Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *