An ɗauki mata 30 aikin koyar da biranya shayar da jaririnta

Spread the love

Gidan ajiyar namun-daji na Dublin Zoo ya ɗauki jerin wasu uwaye masu shayarwa domin tallafa wa wata biranya shayar da jaririnta.

Biranyar mai shekara 19 mai suna Mujur, ta haifi birin ne a ƙarshen watan Yuli amma kuma ba ta iya shayar da shi.

Gidan Zoo ɗin ya nemo mata 30 inda ya nemi su dinga shayar da jariransu a gaban biranyar kafin ta haihu a matsayin wata hanyar horarwa.

Mujur ta taɓa haihuwar birai biyu a 2019 da 2022, amma Zoo ɗin ya ce ba ta nuna “kulawar da ta dace ba a matsayinta na uwa”, kuma dalilin haka ya sa suka mutu.

Biranyar “na nuna sha’awa sosai” idan ta ga matan suna shayar da jariransu ta cikin gilashi, har ma tana kwaikwayon abin da suke yi.

An kuma nuna mata bidiyo na wasu biran suna shayar da jariransu.

A cewar Zoo ɗin, Mujur ta ɗauki darasi sosai amma kuma ba ta iya ɗora shi a bigiren da ya dace domin shayar da jaririn, saboda haka ne aka fara amfani da bulumboti wajen shayar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *