An aiwatar da hukuncin kisa na farko ta hanyar amfani da sinadarin nitrogen a Amurka

Spread the love

Jihar Alabama ta Amurka ta zartar da hukuncin kisa a karo na farko ta hanyar amfani da sinadarin nitrogen kan wani Kenneth Smith da ake rike da shi a gidan yari.

Kenneth Smith da aka samu da laifin kisa, an yanke masa wannan hukunci ne bayan kotun koli ta yi watsi da karar da aka ɗaukaka a gabanta domin nema masa sasauci.

Jami’ai dai na cewa salon kashe shi, sassauci ne a gareshi, yayin da masu suka ke cewa an nuna rashin imani.

An dai biya Smith kuɗi ne ya kashe wata matar wani mai wa’azi, Elizabeth Sennett, inda aka kama shi da laifi kuma aka kama shi tun a cikin shekarar 1989.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

A cewar Cibiyar Bayar da bayani kan Hukuncin kisa, Smith shine mutum na farko da aka kashe ta hanyar amfani da sinadarin iskar nitrogen a duk faɗin duniya.

A jawabinsa na karshe, Smith ya ce kwata-kwata babu tausayi a zuƙatan wasu.

Wata sanarwa, da aka fitar ya ce gwamnar Alabama, Kay Ivey, ta ce wannan hukunci shi ne daidai da abin da Smith ya aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *