Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya bayar da umarnin ƙara yawan jami’an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna, a wani mataki na tsaurara matakai domin inganta zaman lafiya da tsaro a kan titin.
Da yake nuna muhimmancin samar da tsaro domin zirga-zirga a yankin, babban sifeton ‘yan sandan ya ce za a ƙara girke ƙarin jami’an ‘yan sanda da kayan aiki, musamman kayan fasahar zamani da sauran dabarun aiki don inganta tsaro a kan titin.
Mista Egbetokun ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan ƙasa da fasijoji.
Ya ƙara da cewa ganin yawan jami’an tsaron a kan hanyar zai rage ayyukan ‘yan bindigar da ke kai hari a kan hanyar.
Babban sifeton ya yi kiran haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummar garuruwan da ke yankin, yana mai shawartar mutanen su riƙa lura da shige da ficen mutane a garuruwansu, tare da kai rahoton duk wani mutum da ba su yarda da shi ba.
Ya kuma ce ya kamata jama’ar garuruwan su riƙa haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankunansu da na fasinjojin da ke bin hanyar.
Matakin na zuwa ne kwanaki bayan wasu rahotnni sun ce ‘yan bindiga sun tare hanyar a kusa da garin Rijana inda suka sace fasinjoji masu tarin yawa.