Majalisar karamar hukumar Garun Mallam a jihar Kano, ta sanar da ba wa, mazauna kasuwar Kwanar Gafan wa’adin kwana bakwai da su tashi daga cikinta har zuwa wani lokaci anan gaba.
Shugaban karamar hukumar, Hon Barista Aminu Salisu Kadawa ne ya bada umarnin hakan a wajen bikin kaddamar da sake fasalin farfado da tattalin arzikin yankin.
Kadawa ya ce “Duba da irin yadda kasuwar aka mai da ita tamkar wata mafaka ta cibiyar yada badala, maimakon ainihin abun da aka kafa kasuwar tun farko, Sai ga shi an buge da yin abubuwan da suka sha banban da manufar kasuwar.
Haka zalika ya bukaci mazauna kasuwar da su tattara kayansu su bar wajen, kafin ranar 1 ga watan Janairu 2025 domin duk wanda aka kama ya bijirewa umarnin za a hukunta shi.
” mu na fatan jami’an yan sanda za su kama duk wanda ya ketara wannan rana don a kaishi gaban kotu, kuma mun shirya fuskantar duk wani kalubalen shari’a da za a zo mana dashi muma muna da namu lauyan”
” Duk wanda yake da shago a kwanar Gafan , ya zo ya bi ka’idojin wadanda suka kamata ya ba wa shagonsa”.
- Harin Jiragen Sojojin Nigeria Ya Kashe Mutane 10 A Sokoto
- Yan Sandan Kano Sun Gurfanar Da Mutanen Da Ake Zargi Da Addabar Danbatta Da Sace-sace Da Fashin Babura.
Ya kara da cewar nan gaba kadan za a bayyana lokacin da za a yi bikin sake bude ta don ci gaba da kasuwanci iri daban-daban, ba iya na kayan Gona ba, har nau’in sauran ababan more rayuwa.
Daga karshe ya bukaci yankasuwa da su zo don saka jarinsu a kasuwar.
Wani malamin addinin Musulinci, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya yi jawabi akan yadda kasuwar Kwanar Gafan din, ke yin barazana ga tarbiyar yaransu, ya ce abun ba dadin ji balle gani.
Malam Abdullah ya ce “Kasuwar ta zama wajen aikata zinace-zinace ,Luwadi, da yin madigo ga wasu matasa da kuma kawo matan aure kasuwar da daddare, daga nan ya kara da bayyana kasuwar a matsayin wata mafakar barayi da yanfashi da masu safarar muggan kwayoyi.
Imam Abdullahi, ya gode wa shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da ya nuna don kaucewa kara fadawa cikin fushi Allah.
Tun da fari a nasa jawabin, kwamishinan yan sandan Kano, wanda S.A Gusau, ya wakilta ya ce “tuni tunaninsu ya ke kan kasuwar gafan yadda za su kawo karshen mazauna cikinta bayan karewar kayan noman rani, Amma lokaci ya yi da hukumomin tsaro za su sa’ido sa ga masu kunnen kashi.