Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Cp Muhamamd Shehu Dalijan ya mika cekin kudi na fiye da naira miliyan 134 ga iyalai 25 yan sandan da suka rasu a kan aikinsu.
Kudin dai na daya daga cikin alkawuran kyautata walwala da jin dadin iyalan kamar yadda Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya dauka.
Da yake mika musu cakin kudin, Cp Muhamamd Shehu Dalijan ya shawarci iyalan da su tabbatar sun yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.
Yan sanda sun gurfanar da wani mutum bisa zargin yaudara da sace Adaidaita sahu a Kano