Gwamnatin jihar Kano ta bai wa tsofaffin sarakunan masarautun Kano, Rano, Gaya, Bichi da Karaye wa’adin sa’o’i 48 su fice daga fada bayan rushe masarautun da gwamnatin ta yi a yau Alhamis.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da haka lokacin da ya yi jawabi jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta rushe dokar da ta assasa masarautun a shekara ta 2019.
A yau Alhamis ne gwamnan ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano, wadda ta rushe ƙarin masarautu huɗu da aka samar a 2019, wanda hakan ya sanya suka rasa muƙamansu na sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.
Gwamna Abba Kabir ya ce “Ina umartar sarakunan da dokar ta shafa su fice daga fadojin cikin sa’o’i 48”.
Sarakunan da aka sauke su ne:
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero
Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa
Sarkin Gaya Aliyu Ibrahim Abdulkadir
Sarkin Karaye Dr Ibrahim Abubakar
- An mayar da Muhammadu Sanusi II kan muƙamin sarkin Kano
- DSS Ta Bayyana Dalilin Jibge Jami’an Ta A Fadar Sarkin Kano