Wasu Matasa Sun Kone Baburin Adaidita Sahun matasan da Ake Zargin barayin wayoyin jama’a, a asibitin Malam Aminu Kano.
Tunda farko ana Zargin masu Adaidita Sahun, sun dauki wani magidanci da matarsa , har suka kwace musu wayoyi, kamar yadda shaidun gani da Ido suka Bayyana.
Bayan sun kwace wayoyin ne, sai suka Yi Yunkurin guduwa, da Babur din , inda aka tare su a bakin Kofar asibitin, sannan aka bankawa Babur din wuta.
Sai dai rahotanni na cewa matasan da Ake Zargi sun fice daga cikin Babur Adaidita Sahun, suka cika wandunansu da iska.
Kwacen waya a birnin Kano, a Sabon abu bane Amma an jima ba a samu makamancin irin wannan labari ba, sakamakon yadda jami’an Yan Sanda suka dauki mataka magance matsalar.