An bayar da sammacin kama wani lauyan bogi.

Spread the love

Kungiyar lauyoyin a Kenya ta ce an bayar da sammacin kama wani ɗan ƙasar Kenya da ake zargi lauyan bogi ne wanda kuma ke aiki ba tare da shaidar kwarewa ba.

Shari’ar da ake yi masa dai ta ja hankalin ‘yan ƙasar Kenya tun bayan da aka kore shi a matsayin lauya da ke aiki ba bisa ka’ida ba a watan Oktoban bara.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.

A lokacin, jami’an shari’a a Kenya sun buƙaci ‘yan sanda da su kama mutumin, wanda ke aiki da sunan “Brian Mwenda”.

Yan sandan jahar Adamawa da Mafarauta sun cafke wadanda ake zargi da garkuwa da mutane

Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibai

Sun ce mutumin ya sace ainihin sunan wani lauya ne mai suna Brian Mwenda Ntwiga.

Ya mika kansa ga ‘yan sanda jim kaɗan bayan haka.

Daga nan ne aka tuhume shi da laifuka shida, amma ya ki amsa laifinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *