An Cafke Dan Sandan Kotu Na Bogi A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Hamisu Ibrahim, dan shekaru 42 mazaunin kauyen Jangaru, a karamar hukumar Ungoggo ta jahar, bisa zargin sa da bayyana kansa a matsayin jami’in dan sanda, dake aiki a wata kotun dake Ungoggo, tare da karbar kudade a wajen jama’ar da ba suji ba su gani ba.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike da manema labarai a ranar Talata.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce sun samu korafin ne tun a ranar 18 ga watan Nuwamban 2024, da misalin karfe 1:30pm na rana, inda kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya umarci baturen yan sandan Ungoggo, ya tabbatar da an cafko wanda ake zargin.

Binciken yan sanda na farko-farko, ya gano cewar wanda ake zargin, ya karbi kudi daga hannun yan uwan wadanda ake zargi a gaban kotun don ya taimaka mu su wajen karbar belinsu ta hanyar tursasawa.

Rundunar ta yaba wa jami’anta bisa kokarin da suke yi wajen tsaftace aikin dan sanda da kare al’umma don fatattakar batagari dake yunkurin kawo cikas ga aikin yan sanda.

Kwamishinan yan sandan ya yaba wa, al’ummar jahar Kano bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa , inda ya ce da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

a karshe rundunar ta bayar da nambar wayar karta kwana kan wani abu da ba a amince dashi ba, ko sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa 08032419754, 08123821575, 09029292926

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *