An Cafke Wasu Matasa Da Yunkurin Satar Wayar Lantarki, Kwace Da Satar Adaidata Sahu A Gurungawa.

Spread the love

Kwamitin tsaro na bijilanti dake Garin Gurungawa, a karamara hukumar Kumbotso Kano, sun samu nasarar Kama wasu matasa da ake zargi da yunkurin satar wayar lantarki da kuma fashin babur mai kafa uku.

Kwamandan kwamitin tsaron Badamasi Abdullahi, ya ce gungun Matasan sun zo akan Baburin Adaidaita sahu, su shida, wadanda suke zabar unguwar da suka ga alamun babu tsaro a cikin ta.

Jaridar Idongari. ng, ta ruwaito cewa, bayan Matasan sun cire wayar lantarkin wani gida, matar gidan ta yi mu su ihun barayi har aka Kama uku daga cikin su, ya yin da sauran suka tsere.

Matasan da ake zargi sun hada, Ali Shu’aibu Tishama, Abdullahi Muntari Kawon Lambu, Umar Tasi’u Kawo-Tishama .

Sauran sune Garurure, Luti, da kuma Nushi , wadanda suka cika wandunansu da iska.

Shugaban kwamitin tsaron, ya Kara da cewa alamun Matasan ya nuna cewar , sun Saba shigowa yankin domin satar kayan al’umma, inda kuma dubunsu ta cika.

” Bayan mun Kama su , daya a cikin su , ya ce kar a yi masa komai zai fadi gaskiya, Wanda ya tabbatar sa cewa duk Unguwar da suka shiga sai sunga Lalaga suke yin sata, amma da shigowarsu sai suka zargi Kansu sakamakon idanun al’ummar yankin yana kan Masu shiga da fita” Badamasi Abdullahi “.

Matasan Ana zargin sun kware wajen , kwacen wayoyin al’umma, Haura gidaje da kuma fashin Adaidaita sahu.

A karshe ya ce za su mika su hannu hukuma don fadada bincike akansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *