An caka wa wani ɗan jaridar gidan talabijin na Iran wuƙa a wajen gidansa da ke birnin Landan, kamar yadda sanarwar gidan talabijin din ta bayyana.
Gidan talabijin na Iran International Media wanda ya riƙa bayar da rahotannin zanga-zangar da aka yi ta ƙin jinin gwamnatin Iran a 2022, ya ce wata ƙungiya ce ta kai wa Pouria Zeraati mai shekara 36 hari.
‘Yansanda sun ne kwararru kan yaƙi da ta’addanci na ci gaba da bincike kan lamarin.
Jami’an sun ce danjaridar na asibiti a kwance, sai dai ya dawo cikin hayyacinsa.
- Fursunoni 100 Na Neman Afuwa A Kano
- Amarya Ta Zuba Wa Angonta Ruwan Zafi Bayan Ta Yi Yunkurin Daba Masa Wuka.
Idongari.ng Facebook Latsa domin Samun labarai Da Dumi-dumin su