Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, sun ceto wata jaririya ‘yar watanni 14 mai suna Grace Osamagbe, wadda ‘yar aikin gidansu ta sace ta.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umoru Ozigi ne, ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Asabar a Benin.
A cewarsa jami’an tsaro sun kama Rejoice Chukwu, mai shekara 24, da saurayinta Destiny Uchechukwu, mai shekara 28 a Jihar Akwa Ibom.
Ozigi, ya ce masu laifin sun sace jaririyar a Benin kuma sun karɓi kuɗin fansa Naira 160,000.
Duk da haka, bayan sun karɓi kuɗin, sun sayar wa wata mata mai suna Doris Chiwendu, jaririyar a kan kuɗi Naira 500,000.
Bayan gudanar da bincike, ’yan sanda sun gano inda Chiwendu da wata wadda ake zargi, Jane Amaigbo, suka ɓoye jaririyar, wanda suka ceto ta tare da kama su.
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu nan ba da jimawa ba.
- Gwamnatin Nigeria Ta Ceto Mutane 58 Daga Hannun Yan Bindiga
- Gabon na Kada ƙuri’ar raba gardama don amincewa da sabon kundin tsarin mulki