An Ceto Mutane 3 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kubutar da mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a jahohin Kano da Kaduna.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a yau juma’a, ya ce nasarar ta samu ne a yunkurin magance duk wani abu da ya hada da barazanar garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa an samu nasarar biyo bayan umarnin kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,inda  jami’ansu dake yaki da garkuwa da mutane tare da hadin kan yan sandan Bebeji, sun yi bibiya kan garkuwar da aka yi da wani matashi mai suna, Abdulhamid Bello dan shekaru 21, inda suka tsince shi lokacin da ya kwato kansa daga hannun masu garkuwar bayan sun yi masa duka.

Daga bisani yan sandan sun dauke shi zuwa wajen da aka yi garkuwar dashi, a garin Saya-saya dake karamar hukumar Ikkara ta jihar Kaduna,tare da kai farmaki inda aka sake samun wani mai suna ,Musa Idris, dan shekaru 65 an yi garkuwa dashi sannan aka ceto shi.

Lokacin da wadanda ake zargin suka ji motsin yan sanda da kuma farmaki da sukai ne ya sanya suka gudu har suka bar Babur guda 1 da wata Igiya da ake zargin suna daure mutane da ita.

Jami’an yan sandan sun kai su asibiti don duba lafiyarsu.

Haka zalika a ranar 9 ga watan oktoba 2025, yan sandan dake yaki da masu garkuwa da mutane, sun yi nasarar ceto wani matashi mai suna, Ashiru Murtala mai shekaru 19 dan asalin garin Beli dake karamar hukumar Rogo.

Kakakin rundunar yan sandan Kano, ya ce an bi wadanda ake zargin har zuwa Hunkuyi dake jihar Kaduna, inda masu garkuwar suka ajiye shi a cikin gonar Rake suka gudu.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori , ya bayar da umarnin fadada bincike kan lamarin don kamo dukkan wadanda suke da hannun a akata laifukan.
A karshe ya yaba wa jami’an da suka yi aikin tare da godewa al’ummar jihar kan hadin kan da suke bayarwa a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *