Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mata kusan 20 daga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina tare da mika su hannun hukumomin jihar.
Sojojin sun ce sun samu nasarar kubutar da mutanen ne yayin wasu hare-haren da suka kai kan maboyar ‘yan bindigar a dazukan ‘yan-tumaki da Dan-Ali.
Hakan dai na zuwa ne bayan sace wasu mata 53 da ke kan hanyarsu ta zuwa kai amarya a yankin karamar hukumar Sabuwa.
Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna
An fara taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Ecowas
A lokacin da ya yi wa BBC ƙarin bayani, kwamishinan harkokin tsaro na jihar Katsina, Nasir Mu’azu ya ce babu tabbas kan lokacin da aka sace mutanen da aka ceton.
Sai dai ya bayyana cewa mutanen da aka ceton ƴan asalin ƙaramar hukumar Musawa ne da ke jihar.
Ko a makon da ya gabata, wasu ƴan bindiga sun sace ƴan rakiyar amarya sama da 50 a ƙaramar hukumar Sabuwa, waɗanda masu garkuwa da mutanen suka yi barazanar sayar da su da kuma sake aurar da amaryar.