An ci tarar DSTV kan ƙara kuɗi ba tare da izini ba

Spread the love

Kotun Kare Masu Sayayya da Gasa Tsakanin Kamfanoni ta Najeriya ta ci tarar fitaccen kamfanin talbijin na ‘Multichoice’ na tauraron ɗan’adam mamallakan DSTV da GOTV nai miliyan 150, saboda saɓa wa umarnin kotu.

Yayin da suke yanke hukuncin ranar Juma’a, alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Thomas Okusu sun umarci kamfanin ya yi wa ‘yan Najeriya masu hulɗa da shi rajistar kallo kyauta na wata guda.

A baya kotun ta dakatar da kamfanin daga ƙarin kuɗi da ya yi wa abokan hulɗarsa ba tare da cikakkiyar sanarwa ba, bayan da wani lauya Barista Festus Onifade ya shigar da ƙara gaban kotun.

Barista Onifade ya yi iƙirarin cewa sanarwar ƙarin kuɗi na kwana takwas da kamfanin ya bai wa abokan hulɗarsa bai wadatar ba.

Lauyan kamfanin ya gamsu da hukucin da aka yi a baya kan batun iyakance farashi, yayin da shi kuma Onifade ya mayar da hankali kan rashin bayar da isasshen lokaci kan duk wani ƙari da za su yi, maimakon ya yi magana kan ƙara farashin, lamarin da ya sa kotun ta tabbatar da huruminta na sauraron ƙasar, inda ta yanke wa kamfanin hukuncin.

Daga baya dai kotun ta sanya ranar 3 ga watan Yuli domin sauraron ainihin ƙarar da Onfaden ya shigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *