An Dage Ci Gaban Shari’ar Da Wani Mawaki Ya Yi Karar BBCH

Spread the love

Babbar kotun tarayyana dake zamanta a jahar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ta ci gaba da sauraren karar da wani Mawaki , mai suna Abdul Kamal, ya shigar da kafar yada labaran BBC Hausa, bisa zargin yin amfani da sautin wakarsa a shirin daga bakin mai Ita.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan BBC , Barista Micheal Ogoyi, ya roki kotun ta basu damar yin gyae-gyare don yin martani akan da’awar mai karar.

Sai dai lauyan mai karar Barista, Bashir Ibrahim, ya ce za su yi martani akan rokon.

Mai shari’a, Muhammad Nasir Yunusa, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Yuni 2024 kamar yadda jaridar idongari ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *