An dakatar da masu tsaron asibitin Imam Wali bisa zargin sakaci da aiki har mai Nakuda ta haihu a Mota a Kano.

Spread the love

Hukumar kula da asibitoci ta jahar Kano, ta amince da dakatar da masu tsaron asibitin Haihuwa na Imamu Wali, bisa zarginsu da yin sakaci a kan aikinsu, har wata mata mai juna biyu ta ke Nakuda ta haihu a cikin Mota.

Shugaban hukumar kula da asibitocin jahar Kano, Dr. Mansur Mudi Nagode, ne ya bayyana hakan biyo bayan wani faifen bidiyon faruwar lamarin da ya yadu a shafukan sada zumunta.

Idongari.ng ya ruwaito cewa bidiyon ya nuna yadda mijin matar ke neman taimako daga masu gadin Asibitin, ta hanyar kwankwasa kofar Asibitin da kiran neman taimako, amma babu wanda ya kawo masa dauki cikin jami’an da ke tsaron Asibitin , inda hakan ya fusa ta shi ya dauki bidiyon faruwar lamarin tare da yada shi a shafukan sada zumunta.

Nagode ya ce dakatarwar ta zama wajibi, kan sakaci da aikinsu kuma ta fara aiki ne nan ta ke.

Sanarwar da jami’ar yada labaran hukumar kula da asibitocin jajar Samira Suleman, ta fitar ta ce hukumar ba zata bari a dinga yin sakaci da lafiyar al’umma ba.

Koda a ranar 26 ga watan Nuwamban 2023, wata mata mai juna dake nakudar haihuwa ta fuskanci irin wannan yanayi na rashin kasancewar masu gadin Asibitin a kusa , inda mijinta ya mayar da ita zuwa asibitin kwararru na Murtalata Muhammad dake birnin Kano.

Sanarwar ta kara da cewa, an dakatar da wasu jami’an kiwon lafiya uku a bangaren gwaje-gwaje, bisa zarginsu da yin sakaci da karbar kudi da kuma zargin aikata lalata da marasa lafiyar da ba za su iya biyan kudi ba, sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen wadanda aka dakatar din ba.

Nagode ya ce, za a kafa kwamitin da zai yi bincike don ladabtar da duk wanda aka samu ya na da hannu ,dan daukar matakin da ya dace daidai da dokar aikin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *