An dakatar da sanata Ningi daga Majalisar Dattijan Najeriya

Spread the love

Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun ‘zubar da ƙimar majalisar.’

A wani zama cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da kafar yaɗa labaru ta BBC.

Babu sahalewar Buhari a yawancin kuɗaɗen da CBN ya fitar – Fadar shugaban ƙasa

Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattijai kan zargin cushe a kasafin kuɗin 2024

Haka nan an bai wa sanata Ningi damar yin nasa bayanin, inda ya bayyana cewa an yi wa kalaman nasa mummunan fassara ne.

Da farko dai an gabatar da buƙatar dakatar da sanatan na tsawon shekara ɗaya, sai dai daga bisani, sanata Garba Maidoki daga jihar Kebbi ya buƙaci a rage hukuncin zuwa dakatarwa na wata uku, tare da bai wa Ningi damar rubuta takardar neman afuwa.

A ƙarshe majalisar ta cimma matsaya, inda ta yanke wa sanata Ningi dakatarwa ta tsawon wata uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *