An dakatar da yin gwanjon kayan Mandela

Spread the love

An dakatar da wani gwanjon kayayyaki kusan 70 na fitaccen ɗan yaƙi da wariyar launin fata na ƙasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela – waɗanda suka haɗa da na’urar taimaka masa wajen sauraron magana, da sandunan tafiyarsa, da gilashin karatunsa da wasu sauran kayansa da dama.

Gidan gwanjon kaya na Guernsey da ke birnin New York a ƙasar Amurka ya sanar da hakan ne a shafinsa na intanet ba tare da bayar da wani dalili ba, amma hakan ya biyo bayan korafe-korafe da aka yi a Afirka ta Kudu kan batun sayar da kayayyakin nasa.

Likitoci sun dakatar da ayyukansu a Asibitin Murtala da ke Kano

Babbar ‘yar Mandela, Makaziwe Mandela, ta shirya sayar da kayayyakin a wani gwanjo a ranar 22 ga watan Fabrairu, inda ta ce tana son yin amfani da kuɗin ne wajen gina wani wurin tunawa da shi, kusa da inda aka binne shi.

Hukumar kula da al’adun gargajiya ta ƙasar Afirka ta Kudu (Sahra) ta ƙalubalanci aniyar ta Makaziwe Mandela ta sayar da kayan na mahaifinta a gaban kotu, amma ba ta samu nasara ba inda ta kuma ce za ta ɗaukaka ƙara.

Har Yanzu Kuna Tare Da Mu —Martanin ECOWAS Ga Nijar, Mali Da B/Faso

Ministan al’adu na Afirka ta Kudu Zizi Kodwa ya ce hana sayar da kayayyakin Mandela ya zama dole saboda “yana da muhimmanci ga al’adun Afirka ta Kudu”.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato jikan Mandela, Ndaba yana cewa shi ma yana adawa da gwanjon.

Mandela ya rasu a shekara ta 2013 yana da shekaru 95 a duniya.

Ya shafe kusan shekaru 30 a gidan yari saboda yaƙi da mulkin wariya, kuma shi ne baƙar fata na farko a Afirka ta Kudu da ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1994 inda ya sauka daga mulki bayan shekara biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *