An dawo da ƴan Kano kusan 50 da aka yi safara zuwa Ghana

Spread the love

Hukumar yaki da bautarwa da safarar ɗan adam a Najeriya NAPTIP haɗin guiwa da gwamnatin jihar Kano sun yi nasarar dawo da wasu yan jihar 59 da aka yi safararsu zuwa ƙasar gana don samun ingantaciyar rayuwa a chan.

Wadanda aka ceto din dai sun haɗa da maza da mata, da ‘yan mata, da yara ƙanana, inda wasu daga cikinsu sun kai shekaru 17 zuwa 18, yayin da wasu kuma yara basu fi shekaru 3 zuwa 4 ba a duniya.

Hajiya Amina Abdullahi Sani, kwamishinar ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara ta jihar Kano, ta ce an tafi da su ne biyo bayan romon bakan da aka yi musu na samun kyakkyawar rayuwa da kuma samun arziki a Ghana.

“Mun sami takarada cewar ga mutum 59 da aka dawo da su, ciki kuma 47 yan asalin jihar Kano ne, yayin da suran kuma suka futo daga wasu jihohi, don haka muka je muka tabbatar cewa ƴan jiharmu ne, don haka muka dawo da su gida don dauakr mataki na gaba” inji kwamishiniyar.

Ta ce yayin da ake tafiya da wasu Ghana, wasu kuwa ana fasakaurinsu ne zuwa wasu kasashe kamar Libiya, ko Masar da sunan samun aiki don tara abin duniya, daga bisani kuma sai su tsnici kansu a mummunan yanayin bautarwa kamar bayi idan aka fita da su.

Kwamishiniyar Kanon ta ce”Bisa binciken da muka yi, dukkan matan da aka ceto sun fice ne sakamakon yanayin da suka tsinci kansu a ciki na takaicin rashin miji da zai dauki nauyinsu, wasu aure ya mutu, wasu babu mijin ya rasu abubuwa dai irin wadannan”

Ta kuma buƙaci gwamanati da ta kafa wani kwamiti ko wata kotu da za ta rika nemo maza masu guduwa su bar iyalinsu a mummunan yanayi don a rika hukunta su”.

Matsalar bautarwa da safarar bila adama a Najeirya dai matsala ce da aka jima ana fama da ita, wanda tsawon lokaci akan ji hukumar ta NAPTIP na cewar ta ceto yan kasar da ake yunkurin safararsu, tare da kama wasu daga cikin masu safarar mutanen, amma sai dai har yanzu maimakon lamarin ya yi baya, sai ma dai ƙaruwa ma ya ke.

Ana zargin ana dibar yan Najeriya ana kai su kasashen larabawa a gabas ta tsakiya, wasu ma wasu kasashen Afrika da ke fama da yaki domin aikataua, amma daga bisani sai su rika kokawa kan halin da suke shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *