An Fara Bincike Kan Dalilin Da Ya Sanya Jami’in Kwastam Ya Harbe Kansa A Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta ce ta Fara gudanar da bincike kan dalilin da sanya wani jami’in kwastam, mai suna , CSC Abdullahi Abdulwahab Magaji Mazaunin Unguwar Farm Center , ya harbe kan da bindiga kirar Pump Action.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa, da ya fitar a Ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, bayan samun rahotan ne Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura tawagar yan sanda, karkashin jagorancin Baturen yan sandan Farm Center, CSP Ibrahim Abubakar , zuwa wajen da lamarin ya faru.

Jami’in Kwastam din ya hallaka kansa, a Ranar 6 ga watan Mayu 2024 , da misalin karfe 12pm na dare kamar yadda jaridar idongari.ng, ta ruwaito.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya Kara da cewa, yanzu haka batun Yana sashin gudanar da bincike, don gano musabbabin kashe kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *