Gwamnatin Kano ta fara kwashe ‘dubban’ yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar.
Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran.
Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce “mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni.”
“Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba,” in ji Daurawa.
Shugaban na hukumar Hizba ya ce alƙaluman da suke da su sun nuna cewa akwai irin waɗannan yara masu gararamba a kan tituna sama da 5000.
Ya kuma bayyana cewa za a tara yaran da aka kwashe ne a wata cibiya, inda za a tantance su, sannan a san matakan da za a ɗauka.
Kano ce jiha mafi yawan al’umma a arewacin Najeriya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ke da yawan ƙananan yara waɗanda ba su zuwa makaranta.
- Tinubu Na Cikin Manyan Masu Aikata Rashawa A 2024 — Rahoton OCCRP
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Mutane 2,425 Da Zargin Aikata Laifuka A Shekarar 2024
Duk da cewa jihar na daga cikin waɗanda suka sanya hannu kan dokar kare hakkin yara a Najeriya, amma har yanzu akwai dubban yara da ke tallace-tallace ba tare da zuwa makaranta ba, yayin da wasu yaran kuma ke barace-barace a kan tituna da sunan neman ilimin addini.
Sheikh Daurawa ya ce bayan kammala tantance yaran, da inda suka fito, za a sanya wasu daga cikinsu makaranta yayin da za a koya wa wasu sana’a.
Ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar gurfanar da wasu iyayen da aka tsinci yaran nasu na gararamba kan titi, a gaban kotu.
“Wanda ya yi sakaci ya bar ɗansa yana yawo a kan titi duk da cewa yana da halin ɗaukar nauyinsa, to za mu gurfanar da shi a gaban kotu”.
Sai dai ya ce yaran da ba su da iyaye ko waɗanda rikici ya tarwatsa – gwamnatin za ta ɗauki matakin gyara musu rayuwa ta hanyar ba su ilimi da koya musu sana’a.