Gwamnatin Kano ta fara tantancewa tare da yi wa ƴan ƙasashen waje mazauna jihar rajista da irin kasuwancin da suke yi.
An fara rajistar ne daga Kantin Kwari, domin tattara bayanan ƴan ƙasashen waje da suke zaune a jihar da sanin haƙiƙanin irin kasuwancin da suke yi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a jiya Laraba, wasu ƴan ƙasashen waje, musamman ƴan China da India sun je wajen rajistar domin a tantance su.
Sun kai takardu irin ru fasfo da sauran bayanansu, sannan wasu sun zo abokan kasuwancinsu ƴan jihar ta Kano domin tsaya musu.
Barista Tijjani Ahmed Falgore, wanda jami’i ne na ma’aikatar kasuwanci, wanda kuma yake cikin kwamitin rajistar, ya ce wasu ƴan ƙasashen wajen suna zaune ne a ƙasar ba tare da biyan haraji, wanda hakan ne ya sa aka ƙafa kwamitin.
“Maƙasudin shi ne a tantance daɗewarsu a ƙasar da kuma irin kasuwancin da suke yi a Kano,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa akwai sama da ƴan ƙasashen waje 6,000 a Kano.
An kafa kwamitin ne a ƙarƙashin Alhaji Lawal Isa Kibiya, wanda tsohon jami’in shigi da fice.