An ga watan Sallah a Saudiyya

Spread the love

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke alamnat kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.

Shafin Inside the Haramain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kwamitin duba watan ne ya cimma matsaya bayan ɗaukar awanni ana neman wata.

Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar ta Saudiyya.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne sakamakon kwamitin duba watan a Najeriya da sauran ƙasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *