Gwamnatin jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ta ce ta gano wani gidan sayar da jarirai tare da ceto wasu mata masu ciki biyar a garin Umunya da ke yankin karmar hukumar Oyi.
An gano gidan ne a wani sumamen hadin guiwa tsakanin ma’aikatar lafiya da hukumoin tsaron jihar.
EFCC ta gayyaci shugabanin jami’o’in Najeriya da ake karbar kudin makaranatar da dala
Najeriya ta kai wasan ƙarshe a Afcon bayan doke Afirka ta Kudu
Da ya ke bayani ga manema labarai, kwamishinan lafiya a jihar Dr. Afam Obidike ya ce sun gano cewar gidan sayar da yaran na gudanar da harkokinsa ta hanyar basaja a masatyin asibiti, nan kuwa cibiyar safarar jarirai ce.
Ya bayyana sunan gida da “Asibitin Mother Child and Maternity” da ke kan titin jami’ar Tansian, da a Umunya.
Ya ce gidan ba shi da rajista da gwamnatin Anambra, ya na mai na cewar masu aikin jinyar da ke aiki a gidan duk sun tsere.
Kwamishina lafiyar ya kuma ce wadan aka ceto shekarunsu basu ba su wuce 14 zuwa 21 ba. Ya kuma nanata aniyar gwamnan na magance wannan mastala.