An gano kamfanin da ke sayen murafan kwatamin Abuja da aka sace

Spread the love

Ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja ta ce an gano masu sayan ƙarafan murafan hanyoyin ruwa na titunan Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ministan Abuja, Lere Olayinka ya fitar, ya ce wani kamfanin sarrafa ƙarafa mai suna Abuja Steel Company, na cikin waɗanda ake zargi da sayen ƙarafan da ake sacewa.Sanarwar ta ce kamfanin yana kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ne, sannan an gano wasu daga cikin ‘ƙarafan da ake nema’.

“Ana cigaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suke da hannu wajen sacewa da sayarwa da ma sayen ƙarafan.”

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda aka kama ɗin suna ba da haɗin kai a binciken da ake yi, “sannan tuni Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba da umarnin musanya murafan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *