An gano Kurar da ta tsere daga gandun dajin Jos

Spread the love

Rahotanni a Najeriya na cewa an kama kurar da ta tsere daga gandun dajin Jos, lamarin da ya haifar da fargaba da zaman ɗarɗar tsakanin mazauna yankin.

Wata sanarwa da hukumar kula da yawon buɗe ido ta fitar a ranar Talata ta ce bayan shafe lokaci ana farautar kurar an kama ta kuma a raye, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *