An gano wani kogo a duniyar wata

Spread the love

A karon farko masana kimiyya sun gano wani kogo a duniyar wata.

Zurfinsa ya kai mita 100, zai iya zama wurin fakewar mutane, a matsayin wani sansani, kamar yadda masanan suka bayyana.

Sun ce ɗaya ne daga cikin ɗaruruwa da ke ɓoye a duniyar da ba a gano ba.

Ƙasashe sun daɗe suna lalaben matsuguni a duniyar wata, amma sai sun kare masu bincike daga tururi da tsananin zafi da kuma yanayi na sararin samaniya.

Helen Sharman, ƴar sama jannati ta farko a Birtaniya ta shaida wa BBC cewa sabon kogon ya yi kama da sansani mai kyau da ɗan’adam zai iya fakewa, tare da cewa mutane za su iya rayuwa tsawon shekara 20 zuwa 30.

Sai dai ta ce kogon yana da zurfi sosai wanda dole sai ƴan sama jannati sun bi dubaru na yadda za su shiga su fita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *