An goge shafin Facebook na mawaƙi Dauda Kahutu Rarara

Spread the love

Bayanai na cewa an goge shafin fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara daga dandalin Facebook

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi zargin cewa wasu masu amfani da dandalin ne suka riƙa kai ƙorafin shafin nasa ga kamfanin na Facebook,(reporting) bayan ya wallafa wata sabuwar waƙa a shafin nasa da ake zargin ba ta yi wa matasan daɗi ba.

A ‘yan kwanakin nan ne dai mawakin ya fitar da wata sabuwar waƙa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

Waƙar dai ta ƙunshi yabo ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan wasu ayyukan da mawaƙin ke iƙirarin shugaban ya samar wa ƙasar.

An ji yo Rarara cikin wasu baitocin wakar na cewa:

“Tinumbu ya gama mana aiki ba batun ɓoyo”.

“Kananan hukumomi ruhinsu ya dawo”.

”Yanzu talauci ƙyaram, yunwa ƙyaram,

kana security daram-dam-dam, ƴanci daram”.

”Sannu farin cikin ƙasa Tinubu, sai godiya, baba makanike wajen gyara lamba ɗaya”.

Sabuwar waƙar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matasan ƙasar ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke fama da su.

Wannan dalilin ne ya sa suke kallon waƙar tamkar izgili ko zolaya mawaƙin ke yi wa ‘yan ƙasar, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin gangamin kai ƙorafin shafin nasa zuwa ga kamfanin Facebook, domin buƙatar kamfanin ya goge shafin.

Bayan kamar kwana biyu da fara gangamin, Facebook ya goge shafin – mai mabiya fiye da miliyan guda – daga dandalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *