Al’ummar unguwar Kawo dake yankin karamar hukumar Nasarawa Kano, sun gudanar da sallah da addu’o’i domin Samun saukin rayuwa bisa halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Wakilin idongari.ng, ya ruwaito cewa, maza da mata ne suka fito, da safiyar yau Lahadi don yin addu’o’in namen sauki a wajen Allaha Mai yaye dukkan wata damuwa.
An gudanar da sallar da addu’o’in, a filin makarantar Primary Kawo , ne a daidai lokacin da al’ummar Nigeria ke ci gaba da kokawa sakamakon sauye-sauyen da Gwamnatin tarayya ta Yi cikin harda cire tallafin man fetur.