An gudanar da zanga-zangar buƙatar hukunta El-rufai a Kaduna

Spread the love

A ranar Alhamis ne masu zanga-zanga karkashin kungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG) suka yi wa gidan gwamnatn jihar dirar mikiya, inda suke neman a gudanar da bincike tare da kama tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai.

Sun buƙaci gwamna Uba Sani da ya gayyaci jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da sauran hukumomin da abin ya shafa domin su kama El-Rufai tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin gwamnatinsa da tafka almundahana ta kuɗi har Naira biliyan 423.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera wakoki tare rike alluna ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban.

Wasu allunan na ɗauke da rubuce-rubuce da ke cewa ‘Za mu mamaye dukkan hukumomin gamnati don korar duk waɗanda ake tuhuma a cikin rahoton’. ‘A daina ba da duk lamunin da ba a bi ka’ida ba kafin a samu’.

A ranar 30 ga atan Maris din, 2024, Gwamna Uba Sani ya bayyana a wani taro cewa jihar na fuskantar ɗimbin basuka anda ta ce ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

Ya ce sama da kashi 70 na kuɗaɗen da jihar ke samu na tafiya wajen biyan basussukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *