Dandazon mutane ne suka fito a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar tare da buƙatar sojojin Amurka da na sauran ƙasashe su fice daga ƙasar.
Nijar dai tuni taa soke yarjejeniyar soji da Amurka a watan ya gabata, kuma hakan na zuwa ne ‘yan watanni bayan da hukumomin sojin ƙasar suka yanke irin wannan alaƙa da Faransa, inda har ma aka kori dakarun tsohuwar uwar gijiyar tata ta mulkin mallaka da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin daga ƙasar.
Yanzu dai ƙasar tana kusanta kanta ga Rasha domin samun tallafi wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi.
Kuma a ranar Laraba ne ƙwararrun sojoji daga Rasha suka isa domin horas da sojojin ƙasa.
- Yan Sanda Na Binciken Yadda Wani Almajiri Ya fille Kan Karamin Yaro A Kano.
- Yan Sandan Kano Sun Sake Cafke Karin Matasan Yan Daba 61 Dauke Da Makamai Da Miyagun Kwayoyi.